14/2/2020 JUMAA.
Shin ba ka da aure ne a wanann rana ta masoya kuma kana neman samun masoya?
Kimanin mutum miliyan 240 a fadin duniya na shiga intanet domin neman wadanda za su aura, a cewar Statista. Amma kana da masaniyar cewa wasu da dama ba su dacewa da kulla soyayya?
Ga wasu hanyoyin da za su taimaka maka wurin jan hankali da muka tattaro daga Zoe Strimpel mawallafiyar 'The Man Diet' da kuma da Suzie Hayman, kwararriyar mai ba da shawara kan zamantakewa.
Wani mutum ya tallata kansa a allon talla don samun masoyiya.
An daure wata mata da ta bude kofar jirgi a sararin samaniya
Wasu kyawawan hotuna da matasa suka nuna yadda rayuwarsu take.
1. Kar ka fara soyayyar domin 'birgewa'
Idan ka ji ba ka so, ka daina. Idan ba ka son mutun kar ka ci gaba da hulda da shi.
'Jarabawa' na da hadari - tana wahalarwa da gajiyarwa tare da sa mana mummunan zato game da kanmu ko wasu.
2. Bi abin da zuciyarka da nutsu da shi
Idan ka fahimci akwai matsala, to kar ka yi wasa da ita.
Akwai yiwuwar ka yi ta tunanin cewa: 'Laifi na ne'. Babu mamaki su ne matsalar.
3. Bincike ya nuna cewa takaita aika
sakonnin ya fi fa'ida
Hira da daruruwan mutane a lokaci guda na iya gajiyar da kai.
Takaita zancenka zuwa ga mutanen da kake jin dadin yin hakan da su - wadanda ka fi ganin alamun tabbaci daga gare su.
4. Shiga wuraren da mutane suka fi yawa
Ka guji shiga dandalin musamman na soyayya - shiga wuraren da mutane suka fi yawa.
Daga cikin mutane kake samun wanda kake so, saboda a haka sai ka shiga wurin mutanen da suka fi yawa. Kar ka biye wa dandalin masu riya cewa suke da na gari zalla.
Ba za ta yiwu ba. Kuma babu wani yanke.
5. Farawa da neman abokai
Alaka mafi kyau na kulluwa idan ta fara daga abota sannan ta rikide ta koma ta soyayya.
Akwai yiwuwar abokai su yi dalilin haduwar ka da masoyinka.
6. Kasance mai saukin kai
Kana iya tunanin cewa ka san abin da ya fi birge ka amma...
Idan ka fiye tsuke zabinka, akwai yiwuwar ba za ka samu wanda ya dace da kai ba, saboda kawai ba shi da kamannin hakan a fuska.
7. Ka yi hattara da tsanaki.
Babbar illar soyayyar intanet ita ce rashin cikakken masaniya game da juna, saboda kowannenku mutanen da ya sani daban suke da na dayan.
Yi hattara idan har ka ga alamun matsala ko rashin gaskiya.
Rokon kudi daga sabon masoyi - ko yawan saba alkawari - ya isa zama dalilin ka yanke alakar.
Kar ka jefa kanka cikin rashin tabbacin farin ciki a soyayya.
Wannan sako an fassara shi ne daga shirin abokan hulda na BBC wato You & Yours.
Thank's for reading my article
Hanyoyin da zaka samu budurwar aure a intanetCreated at 2020-02-14 19:05:49
Tags:
Intanet
,
soyayyar facebook
,
Valantine
0
Rate upStarShare: