Pair of Vintage Old School Fru
Click here to visit © IBN HUJJAH™ Wap enjoy visiting...
tallace tallace na musanman awannan shafi kashiga koina ba matsala
Click here to visit © OMAR FAROOQ™ Wap enjoy visiting...
click to S M SCoollogo com-6122402
Ameenujibga BlogHomeForum

Ameenu jibga wap
Follow @fabregasjibga Good
¤RAMADAN MUBARAK¤ASSALAM ALAIKUM¤ KUDINGA RUBUTA AMEENUJIBGAWAP.XTGEM.COM A FCBK¤TWITTER¤I.GRAM¤YAHOO¤XTGEM¤DOMIN KAUNA¤
2024-05-03
1

Hanyoyin da zaka samu budurwar aure a intanet

Hanyoyin da zaka samu budurwar aure a intanet
14/2/2020 JUMAA. Shin ba ka da aure ne a wanann rana ta masoya kuma kana neman samun masoya? Kimanin mutum miliyan 240 a fadin duniya na shiga intanet domin neman wadanda za su aura, a cewar Statista. Amma kana da masaniyar cewa wasu da dama ba su dacewa da kulla soyayya? Ga wasu hanyoyin da za su taimaka maka wurin jan hankali da muka tattaro daga Zoe Strimpel mawallafiyar 'The Man Diet' da kuma da Suzie Hayman, kwararriyar mai ba da shawara kan zamantakewa. Wani mutum ya tallata kansa a allon talla don samun masoyiya. An daure wata mata da ta bude kofar jirgi a sararin samaniya Wasu kyawawan hotuna da matasa suka nuna yadda rayuwarsu take. 1. Kar ka fara soyayyar domin 'birgewa' Idan ka ji ba ka so, ka daina. Idan ba ka son mutun kar ka ci gaba da hulda da shi. 'Jarabawa' na da hadari - tana wahalarwa da gajiyarwa tare da sa mana mummunan zato game da kanmu ko wasu. 2. Bi abin da zuciyarka da nutsu da shi Idan ka fahimci akwai matsala, to kar ka yi wasa da ita. Akwai yiwuwar ka yi ta tunanin cewa: 'Laifi na ne'. Babu mamaki su ne matsalar. 3. Bincike ya nuna cewa takaita aika sakonnin ya fi fa'ida Hira da daruruwan mutane a lokaci guda na iya gajiyar da kai. Takaita zancenka zuwa ga mutanen da kake jin dadin yin hakan da su - wadanda ka fi ganin alamun tabbaci daga gare su. 4. Shiga wuraren da mutane suka fi yawa Ka guji shiga dandalin musamman na soyayya - shiga wuraren da mutane suka fi yawa. Daga cikin mutane kake samun wanda kake so, saboda a haka sai ka shiga wurin mutanen da suka fi yawa. Kar ka biye wa dandalin masu riya cewa suke da na gari zalla. Ba za ta yiwu ba. Kuma babu wani yanke. 5. Farawa da neman abokai Alaka mafi kyau na kulluwa idan ta fara daga abota sannan ta rikide ta koma ta soyayya. Akwai yiwuwar abokai su yi dalilin haduwar ka da masoyinka. 6. Kasance mai saukin kai Kana iya tunanin cewa ka san abin da ya fi birge ka amma... Idan ka fiye tsuke zabinka, akwai yiwuwar ba za ka samu wanda ya dace da kai ba, saboda kawai ba shi da kamannin hakan a fuska. 7. Ka yi hattara da tsanaki. Babbar illar soyayyar intanet ita ce rashin cikakken masaniya game da juna, saboda kowannenku mutanen da ya sani daban suke da na dayan. Yi hattara idan har ka ga alamun matsala ko rashin gaskiya. Rokon kudi daga sabon masoyi - ko yawan saba alkawari - ya isa zama dalilin ka yanke alakar. Kar ka jefa kanka cikin rashin tabbacin farin ciki a soyayya. Wannan sako an fassara shi ne daga shirin abokan hulda na BBC wato You & Yours.
Thank's for reading my article Hanyoyin da zaka samu budurwar aure a intanet
Created at 2020-02-14 19:05:49
Tags: Intanet , soyayyar facebook , Valantine

0 Rate upStar
Share: F T G
Back to posts
This post has no comments - be the first one! Hanyoyin da zaka samu budurwar aure a intanet
Hi dear if you like(love) this wapsite and you want yours to be create,design for little amount and earn money per month on your site today click HERE
Kujera33183980 1274480762685550 3635758363742044160 o
¤RAMADAN MUBARAK¤ KUDINGA RUBUTA ¤AMEENUJIBGAWAP.XTGEM.COM A FCBK¤TWITTER¤I.GRAM¤YAHOO¤XTGEM¤DOMIN KAUNA¤
FACEBOOK ARENA UPDATES domin samun tallafi bangaren facebook click HERE
2GO ARENA UPDATES,domin samun agaji akan 2goHERE
Online: 1 user
Today : 6 user
This Week : 27 user
This Month : 17 user
Total all : 21076 visitors
Forum
Blog About Us
Countat Us

ameenujibgawap.xtgem.com™
Site Owned By Ameenu fabregas Jibga
Design By IbnHujjah™
All Rights Reserved © 2018
Created By:AMEENU JIBGA WAP
Copyright © 2016 -
Click here to visit © AMEENU GLOBAL™ Wap enjoy visiting...